![]() |
---|
![]() |
![]() ![]() |
Ƙungiyar Littafi Mai-Tsarki ta Najeriya | |
---|---|
Founded | 1966 |
Classification |
|
Bible Society of Nigeria ( BSN ) kungiya ce mai zaman kanta ta Kirista ba don samun riba ba a Najeriya wacce ke fassara, bugawa da rarraba Littafi Mai-Tsarki na Bayibul a harshen Turanci dama wasu harsunan Najeriya da yawa.[1][2][3][4] An kafa kungiyar a ranar 8 ga watan Fabrairu 1966, an gina ƙungiyar a kan aikin farko na Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki ta Birtaniya da Ƙasashen waje, Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki ta Amirka, da Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki ta Scotland, waɗanda suka fassara kuma suka buga Littafi Mai-Tsarki na Bayibul a cikin harshen Efik a shekarar 1868.[5] Fasto Samuel Adesola Sanusi shine babban sakatare kuma babban jami'in ƙungiyar Bible Society of Nigeria a yanzu.
An kafa kungiyar Bible Society of Nigeria, ranar 8 ga Fabrairun 1966 ta hanyar ƙoƙarin farko na Marigayi Dr. Francis Ezeogo Akanu Ibiam, ɗan asalin yankin na farko na rusasshiyar yankin Gabas. Tun da farko a watan Fabrairu, 1965, Dokta Ibiam ya fara tuntuɓar wakilan yawancin Coci [Kungiyoyin Majami'u) a Najeriya kan buƙatar kafa ƙungiyar Littafi Mai Tsarki na Bayibul ta ƙasa a Najeriya. An yanke shawara gaba ɗaya na waccan taron ne aka kafa kungiyar Bible Society of Nigeria wanda sakamakon haka ya kai ga kafa gami da kaddamar da ita a ranar 8 ga watan Fabrairu 1966. Kafin 1966, Ƙungiyar tana ƙarƙashin kulawar Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki na Bayibul ta Biritaniya da Ƙasashen Waje [BFBS] wadda ta yi aiki a Najeriya tun daga 1807. Sai kuma Littafi Mai Tsarki House, Apapa yana hidima a matsayin cibiyar rarraba wa wasu ƙasashe na Yammacin maƙwabtan Afirka.
Al'ummar wannan ƙungiya na da hedkwatarta a Office Address 18, Wharf Road, Apapa, Jihar Legas, Najeriya. Ofishin kamfani yana a lamba 150, Ikorodu Road, Onipanu, Jihar Legas, Najeriya. Tana da cibiyoyin rarraba Littafin Mai Tsarki na Bayibul a wasu garuruwan Najeriya:
Kungiyar ta fassara Littafi Mai Tsarki na Bayibul, zuwa harsuna 26 na Najeriya.[7][8]
Daga cikin harsuna ashirin da shida (26) da aka fassara Littafin Mai Tsarki na Bayibul sun haɗa da:
Bura
Ƙungiyar Littafi Mai Tsarki na Bayibul ta Najeriya na da gidajen baƙi uku da ke a cikin biranen Najeriya uku ( Lagos, Ibadan da babban birnin tarayyar Abuja ). [11]