![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 17 ga Janairu, 1980 (45 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Makarantar Nahawu ta CMS, Lagos |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi, mai rawa da mai rubuta waka |
Sunan mahaifi | Adigun, Bashorun Gaa, Baale da 9ice |
Artistic movement |
hip-hop (en) ![]() Afrobeats fuji music (en) ![]() |
Kayan kida | murya |
Alexander Abolore Adegbola Akande, wanda aka fi sani da 9ice (an haifeshi ranar 17 ga Janairu 1980), mawakin Najeriya ne, marubuci kuma ɗan rawa. Ya shahara wajen yin amfani da yaren Yarbanci a cikin waƙoƙinsa da kuma waƙoƙin karin magana da salon isar da sako na musamman.
An haifi 9ice a wani gida mai mata biyar da ’ya’ya tara, a Ogbomosho, Jihar Oyo da ke a Yammacin Najeriya. Ya taso ne a unguwar Shomolu Bariga da ke wajen Legas. Ya yi mafarkin zama mawaƙi.[1] Iyayensa sun gano basirarsa ta waƙa, kuma suka yanke shawarar ba shi damar zama mawaƙi.[2][3]
A cikin 1996, 9ice ya yi rikodin demo na farko, mai taken "Risi de Alagbaja", amma sai a shekara ta 2000 ya fito da waƙar solo na farko, "Little Money".[4][3]
A cikin 2008, 9ice ya fitar da waƙar "Gongo Aso". Waƙar da ta samu karɓuwa, an nemi 9ice ya yi wasa a wurin bikin 90th Birthday Tribute na Nelson Mandela a London a watan Yuni 2008.[5] Ya ci gaba da lashe kyautar gwarzon mawakin salon Hip Hop na shekara a MTV Africa Music Awards.[6][7]
"Gongo Aso" ya saka shi ya lashe lambar yabo guda hudu a gasar Hip Hop World Awards na 2009 da aka gudanar a International Conference Centre, Abuja : Album of the Year, Artite of the Year, Song of the Year da Best Rap in Pop Album.[8]
A cikin 2020, 9ice ya sake fitar da wani kundi, Tip of the Iceberg: Episode 1.[9]
Shi ne wanda ya kafa kuma Shugaba na alamar rikodin Alapomeji Ancestral Record.