Abdul-ƙadir Kure

Abdul-ƙadir Kure
Gwamnan jahar Niger

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Habibu Idris Shuaibu - Mu’azu Babangida Aliyu
Rayuwa
Haihuwa Lapai, 26 ga Faburairu, 1956
ƙasa Najeriya
Mutuwa Jamus, 8 ga Janairu, 2017
Yanayin mutuwa  (cuta)
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

An haifi Abdulkadir Kure a garin Lapai da ke jihar Neja a Najeriya a ranar 26 ga Fabrairu, 1956. Ya yi gwamnan jihar Neja tsakanin 1999 zuwa 2007

Kure  ya yi karatun a fannin civil engineering jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ya kammala digirinsa na farko a shekarar 1976, ya yi NYSC a jihar Benuwe daga 1976-1977, Kure ya fara aiki da ma'aikatar ayyuka ta jihar Neja a matsayin dalibin injiniyan kafin yaci gabada karatun Masters a University of Newcastle, United Kingdom,1981

Aiki da Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan kammala karatunsa, Kure ya koma ma’aikatan gwamnati na jihar Neja, daga baya kuma ya bar aikin hukumar raya babban birnin tarayya Abuja a matsayin babban injiniya a shekarar 1985. Ya yi ritaya daga FCDA a shekarar 1995 a matsayin director of engineering.

Kure ya kasance dan jam’iyyar PDP, wanda a karkashinta ya yi gwamnan jihar Neja daga 1999 zuwa 2007. Ya kasance mai kare shari’ar Musulunci kuma ya kasance gwamna na biyu bayan Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima. gabatar da dokar a Najeriya a watan Mayun 2000. Hakan baiyiwa Kiristocin jihar dadi ba domin suna gani hakan kamar wata hanyace ta mayar dasu Saniyar ware.

Bayan karewar wa'adin mulkinsa shugaban kasa Umaru 'Yar'aduwa ya nada shi shugaban hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) inda ya yi aiki har zuwa shekarar 2010. Tsohon gwamnan ya kasance dan jam'iyyar PDP mai kishin kasa. Ya kasance wakili a babban taron kasa na 2014 da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kira. Ya kuma kasance wanda bai fito fili ya yi tunanin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba a cikin zazzafar gudun hijirar ‘ya’yan Jam'iyyar PDP suke zuwa jam’iyya mai mulki a yanzu.[1]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Kure  ya auri Zainab Abdulkadir Kure, tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati tun shekarar 2007 tana ‘yar majalisar dattawan Najeriya. su n haifi mata biyu mata da maza hudu.[2]

Kure ya rasu ne a ranar 8 ga Janairu, 2017  a kasar Jamus inda ya je neman magani.[3]