Abdul Mshelia

Abdul Mshelia
Gwamnan Jihar Bauchi

ga Augusta, 1998 - Mayu 1999
Theophilus Bamigboye (en) Fassara - Adamu Mu'azu
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Wing Commander (Mai ritaya) Abdul Adamu Mshelia yayi mulki a jihar Bauchi, Najeriya daga watan Agustan 1998 zuwa Mayun 1999 a zamanin mulkin Janar Abdulsalami Abubakar.[1] Lokacin da ya karɓi ragamar mulkin Bauchi uku ne kawai ƙananan hukumomi 20 ke da wutar lantarki.[2] Mshelia ya yi gyare-gyare kaɗan a tsawon wa’adinsa na mulki, amma ya gudanar da zaɓen gwamnatin farko a Jamhuriyyar Najeriya ta huɗu cikin nasara, inda ya miƙa wa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu a ranar 29 ga watan Mayun 1999.[3] A cikin watan Yunin 1999 an buƙaci Mshelia ya yi ritaya, kamar yadda aka buƙaci dukkan tsoffin shugabannin sojoji.[4]