Abdul Rahman Khleifawi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Damascus, 1930 |
ƙasa | Siriya |
Mutuwa | 14 ga Maris, 2009 |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da soja |
Digiri | Janar |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Ba'ath Party (en) |
Abdul Rahman Khleifawi:,( Larabci: عبد الرحمن خليفاوي, romanized: ʿAbd ar-Raḥmān Khulayfāwiyy - 14 Maris 2009), jami'in sojan Siriya ne kuma ɗan siyasa. Ya kasance Fira Ministan Siriya daga 1971 ya gaji Hafez al-Assad wanda ya zama shugaban Ƙasar Siriya zuwa 1972 na tsawon shekara 1 kuma daga 1976 zuwa 1978 na kimanin shekaru 2, ya zama Firayim Minista na wa'adi biyu tare a karkashin, Shugaba Hafez al-Assad.
An haifi Khleifawi a shekara ta 1930. [1] Shi ɗan asalin Aljeriya ne, asalinsa daga Draâ Ben Khedda .[2]
Khleifawi babban soja ne. [3] Ya yi aiki sau biyu a matsayin firaministan kasar Syria. Ya fara mulki daga ranar 3 ga Afrilu 1971 zuwa 21 ga Disamba 1972, a matsayin firayim minista na farko a karkashin shugabancin Hafez al-Assad .[3] Khleifawi ya sake zama Firayim Minista daga 7 ga Agusta 1976 zuwa 27 Maris 1978. [1] Ya kuma taba rike mukamin ministan harkokin cikin gida tsakanin shekarar 1970 zuwa 1971 karkashin shugaba Ahmad al-Khatib da firaminista Hafez al-Assad.
Khleifawi ya rasu a ranar 14 ga watan Maris, shekarar 2009.[4]