Abdulaziz Usman

Abdulaziz Usman
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2011 - ga Yuni, 2015
District: Jigawa North-East
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Jigawa North-East
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Janairu, 1962 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Abdulaziz Usman Tarabu (An haife shi a ranar 1 ga watan janairu, a shekara ta alif 1962) ɗan majalisar dattawan Najeriya ne mai wakiltar jam'iyyar PDP a jihar Jigawa. Ya zama dan majalisar dattawan Najeriya a shekarar 2007.[1]

Abdulaziz Usman yana da digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci.[2] Kafin shiga siyasa, ya kasance babban jami’in tsare-tsare a harkar noma da raya karkara ta Jihar Jigawa. An zabe shi a matsayin memba na Majalisar Wakilai daga shekara ta alif 1999 zuwa shekarar, 2003, kuma an sake zaɓe shi a shekarar, 2003-zuwa shekarar 2007.[1]

A shekarar, 2005, ya goyi bayan Atiku Abubakar, wanda shine mataimakin shugaban kasar Najeriya a lokacin, a wani zargin batanci ga mujallar Newswatch da ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, a lokacin da Atiku ke shugabantar majalisar zartarwa ta kasa.[3]

Aikin majalisar dattawa

[gyara sashe | gyara masomin]

An zabi Abdulaziz Usman ɗan majalisar dattawa ta ƙasa mai wakiltar mazaɓar Jigawa ta arewa maso gabas a shekarar, 2007.[1] Wani rahoto da jaridar This Day ta fitar a watan Mayun na shekarar, 2009 ya ce bai dauki nauyin wani kudiri ba, duk da cewa yana daukar nauyin wasu kudirori, wani lokacin kuma yana ba da gudummawa wajen muhawara a zauren majalisar. Ya kasance shugaban kwamitin kula da harkokin majalisar dokoki.[4][5] A zaben watan Afrilun shekara ta, 2011 ya sake zabensa a matsayin Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas a jam'iyyar PDP, da kuri'u, 135,202.[6]

Samfuri:Nigerian Senators of the 6th National Assembly