![]() | ||||
---|---|---|---|---|
aspect in a geographic region (en) ![]() | ||||
Bayanai | ||||
Ƙaramin ɓangare na | Abubuwan da suka shafi muhalli | |||
Facet of (en) ![]() | Abubuwan da suka shafi muhalli | |||
Ƙasa | Turkmenistan | |||
Wuri | ||||
|
Abubuwan da suka shafi muhalli a Turkmenistan sun fi fitowa fili a wurare uku masu mahimmanci: Kwararowar hamada da bushewar Tekun Aral da kuma gurbacewar sinadarai. Dukkan wadannan yankuna uku suna da alaka kai tsaye da ayyukan noma a kasar.[1]
Hamadar Sahara ce kawai aa yankin karin bayani Afirka ke da yawan hamada fiye da na hamadar tsakiyar Asiya. Sannan Kuma Daga cikin waɗannan, Hamadar Karakum da Hamadar Kyzyl Kum a Turkmenistan suna girma da ɗaruruwan kadada a kowace shekara. Waɗannan sharuɗɗan suna cigaba da kasancewa saboda rashin ingantaccen aikin noma da tsarin kiwo, wanda ya haifar da kasa na yin gishiri-gishiri ƙasa tare da kawar da tsire-tsire na ƙasa bi-da-bi.[2]
Hanyoyin ban ruwa marasa inganci a kan Amu Darya su ma suna taimakawa wajen cigaba da bushewar Tekun Aral.[3][4] Lardin Daşoguz ya fi fuskantar matsaloli sakamakon wannan bushewar. Ingancin ruwan sha ya ragu, kuma matakan ƙwayoyin cuta a cikin ruwa sun ƙaru, kuma adadin mace-macen jarirai da ciwon hanta da rashin lafiya sun ƙaru.[5]
Yawan amfani da taki a kan auduga da sauran amfanin gona, da kuma amfani da magungunan kashe qwari irin su DDT na haifar da babbar matsalar gurbacewar sinadarai. Sannan Yawancin takin zamani da magungunan kashe qwari sun shiga cikin ruwa na ƙasa ta hanyar "leaching" ko zubar da ruwa daga gonaki saboda wuce gona da iri ko amfani da su ta yadda bai dace ba.[6]
Kimanin dala biliyan 6 na "methane" , iskar gas da ke haifar da sauyin yanayi, an yi kiyasin za ta zubar a shekarar 2019/20.[7]
Kasar na hada kai da Tarayyar Turai da kasashe mambobinta da kuma kungiyar tsaro da hadin gwiwa a Turai (OSCE) don ragewa da sarrafa tasirin wadannan matsalolin muhalli. [8][9]