Adama Jarjue | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Gambiya, 12 Disamba 1997 (26 shekaru) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Adama Jarjue (An haife shi a ranar 12 ga watan Disamba 1997) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke buga wa FK Sloga Kraljevo, wasa bayan ya buga wa FK Zlatibor Čajetina wasa a SuperLiga Serbian.
Ya taka leda a kungiyar Gamtel FC ta kasar Gambia [1] har sai da ya sanya hannu tare da sabuwar kungiyar FK Zlatibor Čajetina ta Serbia Top League a lokacin bazara ta shekarar 2020. [2] [3]
A watan Satumba 2015 ya riga ya kasance cikin tawagar kwallon kafa ta Gambia ta 'yan kasa da shekaru 20. [4]
Ya kasance yana cikin tawagar kwallon kafar Gambia ta kasa da kasa da shekaru 23 a ranar 17 ga watan Mayu, 2018, a wasan da suka buga da Morocco. [5]
Ya kasance wanda ba a yi amfani da shi ba a wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Gambia da Najeriya ranar 5 ga watan Yuni, 2021. [6]