Adelina Amélia Lopes Vieira (1850 - 1922 ko 1933) mawakiyar shayari ce ta Brazil, marubuciyar wasan kwaikwayo kuma marubuciyar labaran yara.
An haife ta a Lisbon, ta dawo Brazil tun tana ƙarama,[1] kuma ta kammala karatu a matsayin malama a daf da shekarar 1870.[2] Sun rubuta Contos Infantis (1886) tare da 'yar'uwarta Julia Lopes de Almeida.[1] A shekara ta 1899 ta ba da gudummawa ga A Mensageira, mujallar wallafe-wallafen da Presciliana Duarte de Almeida ta gyara wanda aka yi dona matan Brazil. A farkon karni na ashirin ta rubuta kuma ta fassara wasanni da yawa.[2]