Adeoye Lambo

Adeoye Lambo
Rayuwa
Haihuwa Abeokuta, 29 ga Maris, 1923
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 13 ga Maris, 2004
Karatu
Makaranta University of Birmingham (en) Fassara
King's College London (en) Fassara
Baptist Boys' High School
Thesis Observation on the role of cultural factors in paranoid psychosis among the Yoruba tribe : a study in comparative psychiatry
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a psychiatrist (en) Fassara
Kyaututtuka
Mamba The World Academy of Sciences (en) Fassara

Thomas Adeoye Lambo, OBE (an haife shine a ranar 29 ga watan Maris din shekara ta 1923 - ya mutu a 13 ga watan Maris a shekara ta 2004) ya kasance masani ne kuma ɗan Nijeriya, ne mai gudanarwa kuma likitan mahaukata. ne Shi ne ake ambato a matsayin wanda ya fara samun horon zama a likitan mahaukata na farko a shiyyar yammacin Afirka da kuma Najeriya. baki daya Tsakanin shekara ta 1971 da 1988, ya yi aiki a Hukumar Lafiya ta Duniya, inda har ya kai ga zama Mataimakin Darakta Janar na hukumar.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Lambo a garin Abeokuta na jihar Ogun . Ya halarci wata shahararriyar makaranta mai suna Baptist Boys 'High School, Abeokuta daga shekara ta 1935 zuwa 1940. Daga nan ya wuce zuwa Jami'ar Birmingham, inda ya karanci likitanci. Don ci gaba da karatunsa kuma ya zama kwararre, a shekara ta 1952, ya shiga Cibiyar Nazarin Lafiya, King's College London. Adeoye Lambo lokaci daya ya zama shahararre saboda aikinsa kan ilimin halin tababbu da na tabin hankali.