African Business | |
---|---|
Mujalla | |
Bayanai | |
Farawa | 1982 |
Laƙabi | African Business |
Ƙasa da aka fara | Birtaniya |
Harshen aiki ko suna | Turanci |
Lokacin farawa | ga Janairu, 1982 |
Ranar wallafa | ga Janairu, 1982 |
Shafin yanar gizo | africanbusinessmagazine.com |
Afircan Business mujallar kasuwanci ce ta Afirka wadda kamfanin IC Publications, dake birnin London, ke bugawa.[1] Editan ta, mai ci a yanzu shine David Thomas.[2][3]
An fara buga labarai na jaridar a cikin watan Janairu 1982.[4] Anver Versi shine editan mujallar na farko.[5][6] Hedkwatarta tana a birnin Landan.[7] Mujallar wacce ake wallafa labarai a wata-wata tana taɓo batutuwan kasuwanci a faɗin kasashen Afirka. Rahotanni na musamman sun tattauna takamaiman sassa da masana'antu.[8] Tun daga shekara ta 2012, mujallar na da masu biyan kuɗi-(subscribers) kusan dubu 140,000.[9] Ana buga mujallar da harshen Turanci da kuma Faransanci.[10]
Mujallar na shirya taro duk shekara-shekara na "African Business Awards" tare da haɗin gwiwar Majalisar Kasuwancin Commonwealth. Taron shekara ta 2011, an gudanar da shi a birnin London, na ƙasar Ingila.[11]