Agbor | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jahar Delta | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | 055 |
Agbor itace birni mafi yawan jama'a na tsakanin mutanen Ika. Ta kunshi kabilar Igbo na Anioma. Tana cikin karamar hukumar Ika ta kudu a jihar Delta, a shiyyar siyasa ta kudu maso kudancin Najeriya, yammacin Afrika. Agbor hedkwatar karamar hukumar Ika ta kudu ce a jihar Delta, Najeriya .
Gyaran Kwalejin Ilimi na shekarar 2021 ta sa an mayar da Agbor matsayin birnin kwaleji.
|
Agbor gida ce ga cibiyoyin ilimi da dama. Wasu daga cikinsu sun hada da Jami'ar Delta, Agbor (tsohuwar Kwalejin Ilimi, Agbor); Makarantar Jiyya da Ungozoma ta Jiha, Agbor; Kwalejin Fasaha ta Agbor, Agbor; da kuma shirin Anioma Open University, Agbor.