![]() | |||
---|---|---|---|
2023 - ← Darius Ishaku | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jahar Taraba, 12 Nuwamba, 1970 (54 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Ibadan Jami'ar Jihar Delta, Abraka Jami'ar Tsaron Nijeriya | ||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||
Imani | |||
Addini | Kiristanci | ||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Agbu Kefas (an haife shi ranar 12 ga watan Nuwamba 1970[ana buƙatar hujja]) ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon sojan Najeriya Laftanar Kanal mai ritaya wanda shine gwannan Jihar Taraba tun ran 29 ga watan mayu shekarar 2023 bayan da aka rantsar dashi.[1]
An haifi Agbu Kefas a ranar 12 ga Nuwamba shekarar 1970, a Wukari, Jihar Taraba tsohuwar (jihar Gongola), Najeriya ga dangin Mr. da Mrs. Kefas.[ana buƙatar hujja] [ana buƙatar hujja] sananne ne saboda ya samu ci gaba da nasarori a aikin soja. Ya samu takardar shaidar kammala karatun jami'a daga Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA) da ke Jihar Kaduna inda ya sami digiri na farko a Kimiyyar Siyasa da Nazarin Tsaro a shekarar 1994, Jami'ar Ibadan ta Jihar Oyo, inda ya yi digiri na biyu a fannin shari'a da ilimin halayyar ɗan Adam a shekarar 2005 da Jami'ar Jihar Delta, Abraka inda ya samu digirin digirgir a fannin harkokin gwamnati a shekarar 2008. Hakanan, yana da manyan takardun shedar ilimin zartarwa daga cibiyoyin Ilimi na duniya kamar Harvard Kennedy School a Amurka.[2][3][4]
Agbu Kefas ya yi ritaya daga aikin sojan Najeriya bayan ya shafe shekaru 21 yana aiki. Bayan ya yi ritaya, an naɗa shi shugaban hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015. Ya kuma kasance mamba a kwamitin shugaban ƙasa kan shirin Arewa-maso-Gabas daga shekarar 2016 zuwa 2019 kafin ya shiga siyasa gadan-gadan inda ya zama shugaban jam'iyyar PDP na jihar Taraba a shekarar 2020. A shekarar 2022, Agbu Kefas ya tsaya takara a zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Taraba, ya kuma yi nasara. Kefas ya tsaya takarar gwamnan jihar Taraba a watan Maris a shekarar 2023 a matsayin ɗan jam’iyyar PDP, wadda itace jam’iyya mai mulki a jihar. Ya samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a cikin shekarar 2023 wanda hakan ya bashi damar zama zaɓaɓɓen gwamnan jihar Taraba, inda ya doke Muhammad Yahaya na jam’iyyar NNPP na biyu da ƙuri’u 100,337 kacal. Duk da cewa wasu masu sanya ido akan zaɓen suna ganin an tafka maguɗi sosai wanda har akayi ikirarin cewa abokin takararsa Muhammad Yahaya shine ya lashe zaɓen, amma saboda manyan ƴan siyasar basa sonshi, da kuma kasancewar addini yayi tasiri sosai a zaɓen.
Agbu ya auri Patience kuma suna da ‘ya’ya hudu (4).[5]