Agnese Grigio | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Albignasego (en) , 12 ga Janairu, 1963 (61 shekaru) |
ƙasa | Italiya |
Karatu | |
Harsuna | Italiyanci |
Sana'a | |
Sana'a | Paralympic athlete (en) |
Agnese Grigio (an haife ta 12 Janairu 1963 Albignasego) ita makauniyace ce 'yar wasan Paralympic ta kasar Italiya. Ta samu lambar azurfa da tagulla.[1]
Ta ci gaba a matsayin 'yar wasan pentathlete, kuma mai tseren tsaka-tsaki. Ta yi wasa a gasar wasannin nakasassu ta bazara ta 1984 da akayi a New York, inda ta lashe lambar tagulla a tseren mita 800 B3,[2] da lambar azurfa a Pentathlon B3.[3][4]
Saboda wasu 'yan dalilai, ba da daɗewa ba ta katse ayyukanta na motsa jiki, ta ci gaba da yin wasan motsa jiki (wani horon da ba a cikin Paralympics), a matakin ƙasa da ƙasa.
Ita ce 'yar uwar Emanuela Grigio.