Ahmed Nuhu Bamalli | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Zariya, 8 ga Yuni, 1966 (58 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Hausawa |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Mai wanzar da zaman lafiya |
Ahmed Nuhu Bamalli (an haife shi takwas 8 ga watan Yuni, shekara ta alif ɗari tara da sittin da shida 1966), miladiya.
jami'in diflomasiyya ne na Najeriya, Banki, basaraken gargajiya kuma lauya sannan tsohon jakadan najeriya a kasar Thailand wanda shi ne Sarkin Zazzau na goma sha tara 19, masarautar gargajiya a Najeriya da ke da hedikwata a Zariya, Jihar Kaduna, Najeriya. Shi ne Sarki na farko daga gidan Mallawa da ke mulki tun bayan barin mulki a hannun gidan tsawon ƙarni daya baya, biyo bayan rasuwar sarkin lokacin a shekarar alif dubu daya da dari tara da ashirin 1920,(shekara dari 100 baya), ga kakansa, Sarki Alu Dan Sidi.
An haifi Ahmed a garin Kwarbai Zaria, jihar Kaduna, Najeriya. Shine ɗan fari ga Nuhu Bamalli . Ahmed ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya samu lambar (LLB) a shekara ta alif dubu daya da dari tara da tamanin da tara 1989, sannan ya yi Digiri na biyu a kan Harkokin Ƙasa da Ƙasa da diflomasiyya daga jami'ar a shekara ta alif dubu biyu da biyu 2002. Ya sami difloma a fannin gudanarwa daga jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu a shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da takwas 1998.
Ahmed yayi karatu a ɓangare da yawa na duniya; misali kan warware rikice-rikice a Jami'ar York (Birtaniya) a cikin shekarar alif dubu biyu da tara 2009, Yayi Diploma a fannin jagoranci daga Jami'ar Oxford (UK) a shekara ta alif 2015. Ya kuma sami GMP daga jami'ar Harvard Business School, a shekara ta 2011.
Ahmed shi ne sarki na farko daga gidan mulkin Mallawa a cikin shekaru 100, bayan rasuwar Alh Shehu Idris.
Ya yi aiki a harkar banki kuma a matsayin Babban Darakta sannan daga baya ya rike mukamin Manajan Darakta na Kamfanin Kula da Tsaro da ɗab'i da ma'adanai na Najeriya.
Ya kasance kwamishina na dindindin a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna a shekarar alif dubu biyu da goma sha biyar 2015. Har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin sabon sarkin Zazzau, Ahmed ya rike sarautar Magajin Garin Zazzau kuma ya yi aiki a matsayin Jakadan Najeriya a Thailand, tare da amincewa da Myanmar a lokaci guda.
Ya zama sabon sarkin Zazzau a ranar bakwai 7 ga watan Oktoba,shekara ta alif dubu biyu da ashirin 2020. Shine ɗan fari na Nuhu Bamalli (Magajin Garin Zazzau).