Mejo Aishatou Ousmane Issaka, mataimakiyar darekta ta hulda da jama'a a asibitin sojojo dake Niamey babban birnin Jamhuriyar Nijar, tana ɗaya daga cikin mata sojoji a ƙasar. A shekarar 2016 ta karbi kyautar karramawa da ake ba mata sojoji daga majalisar dinkin duniya saboda aikin da tayi na wanzar da zaman lafiya da tayi a garin Gao na kasar Mali tsakanin shekarar 2014–2015. Tarike kaftin a bangaren shiga tsakanin Jami'an tsaro da fararen hula.[1][2][3]
A ranar 29 ga watan maris, shekarar 2017, Issaka ta karɓi kyauta akan karfafa guiwar mata da kuma take musamman ma saboda aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen Nijar da Mali daga ofishin uwargidan shugaban Amurika Malenia Trumph karkashin jagorancin sakataren hukumar kula da harkokin siyasa ta Amurika Thomas A. Shannon.[4][5][6].