Akshata Murty | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Hubballi (en) , ga Afirilu, 1980 (44 shekaru) | ||||
ƙasa | Indiya | ||||
Ƴan uwa | |||||
Mahaifi | N. R. Narayana Murthy | ||||
Mahaifiya | Sudha Murthy | ||||
Abokiyar zama | Rishi Sunak (30 ga Augusta, 2009 - | ||||
Ahali | Rohan Murthy (en) | ||||
Ƴan uwa |
view
| ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Baldwin Girls High School (en) 1998) Fashion Institute of Design & Merchandising (en) Claremont McKenna College (en) (1998 - 2002) : ikonomi, Faransanci Jami'ar Stanford (2004 - 2006) Master of Business Administration (en) | ||||
Matakin karatu | Master of Business Administration (en) | ||||
Harsuna |
Faransanci Turanci Harshen Hindu Kannada | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Mai tsara tufafi da manager (en) | ||||
Employers |
Infosys (en) Jamie Oliver (mul) Wendy's (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Hinduism (en) | ||||
IMDb | nm13641361 |
Akshata Narayan Murty (An haifeta a watan Afrilu a 1980) magajiya ce 'yar kasar Indiya, 'yar kasuwa, mai kawata kaya kuma 'yar jari hujja ce. Tana auren Rishi Sunak, firaministan Ingila kuma shugaban jam'iyyar Conservative. A cewar jaridar Sunday Times Rich Lis, Murty da Sunak su ne 222 a jerin masu kudi a Birtaniya a shekarar 2022, suna da jimillar dukiya fam miliyan 730 wanda yayi daidai da dala miliyan 830.[1] [2] Ita diyar N. R. Narayana Murty, wanda ya kirkiro kamfanin Infosys da kuma Sudha Murty. Tana kashi 0.93 na hannun jari a kamfanin Infosys tare kuma da wasu hannayen jari a wasu kamfanonin kasuwanci na kasar Birtaniya.[3] [4] [5]
An haife Akshata Murty a watan Afrilu a shekarar 1980 a Hubil dake a kasar Indiya, [6] [7] kakanninta na bangaren uwa suka reneta, lokacin mahaifinta N. R. Narayana Murty da mahaifiyarta Sudha Murty suna aikin kafa kamfanin fasaha na Infosys.[8] [9] Mahifiyarta itace mace ta farko injiniya da tayi ma kamfanin TATA Engineering da Locomotive a lokacin shine babban kamfanin kera mota na kasar Indiya, daga bisani ta zama mai taimakon mutane.[10] Murty nada dan uwa guda daya, Rohan Murty, [11] sun girma a Jayanagar ne wanda yake a wajen garin Bangalore.[12] A shekarun 1990, [13] Murty tayi karatu a babbar makarantar mata Baldwin dake a Bangalore, a shekarar 1980 tayi karatun tattalin arziki da kuma harshen Faransanci a kwalejin Claremont McKenna dake Kalifoniya a dake kasar Amurka. [14] Tana da difloma a kan kera tafafi daga Fashion Institute of Design and Merchandising, [15] da kuma digiri na biyu a kan yadda ake kasuwanci daga jami'ar Stanford.[16]