![]() | ||||
---|---|---|---|---|
position (en) ![]() | ||||
![]() | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya da Masarautar Oyo | |||
Applies to jurisdiction (en) ![]() | Oyo | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Oyo |
Alaafin, ko kuma mai kula da fada a yaren Yarbawa, shi ne sarautar sarkin daular Oyo ta tsakiya[1] da kuma garin Oyo na yammacin Afirka a yau. Take ko Suna ne, na musamman na Oba (sarkin) na Oyo.[2] Wani lokaci ana fassara kalmar a matsayin “sarki”. Sarkin Oyo ya mulki tsohuwar daular Oyo, wadda ta taso daga jamhuriyar Benin ta yau zuwa Najeriya, wadda ta samo asali daga jihohin Kudu maso Gabas da Yamma zuwa Arewa. Mutanen da ke ƙarƙashinsa ana kiransu Yarabawa kuma suna magana da harshen Yarbanci.
Alaafin na Oyo a gargajiyance da Tarihin Yarabawa ance ɗaya ne daga cikin jikoki bakwai na Oduduwa waɗanda daga baya suka zama Sarakuna, wanda ya zama ginshikin tubalin wayewar Yarbawa.[1]
Alafin da Oyo Mesi ne suka kafa gwamnatin tsakiya ta Masarautar. Karamar hukumar ta kasance a hannun oba (idan aka yi masa rawani) ko bale (idan bai cancanci sanya rawani ba).[3] Dangantakar da ke tsakanin Alafin da Obas ta fada ce, wato don mulkinsa da kare shi, Obas, Bales da sarakunan jahohin vassal suna bin sa sau da kafa a dokance.[4] A farkon shekarun 1800, duk da haka, rikice-rikice tsakanin Sarkin Oyo (alafin) da sarakunan gado (obas) na manyan jihohin birni, waɗanda suka ƙunshi majalisar zartarwa mai zaman kanta (oyo mesi), sun raunana ikon tsakiya- kamar Masarautar Oyo ta fara rasa iko a kan masarautu da ke lungu da saƙo da ma birane.[5]
An ci gaba da riƙe wannan lakabin bayan rushewar daular Oyo a matsayin taken sarautar ’yan asalin Oyo, Najeriya a hukumance. Alaafin shine shugaban siyasa na kabilar Yarbawa kuma shine sarki ɗaya tilo da ke da ikon da ake bukata kafin ya naɗa sarki mai wakiltar kasar Yarabawa baki ɗaya.[6] Misalan irin wannan naɗin sun haɗa da Aare Ona Kakanfo na kasar Yarbawa da Iyalode na kasar Yarbawa.
Kamar na shekarar 2021 Alaafin (Sarkin) na Oyo shine Oba Lamidi Adeyemi III wanda shine Alaafin na 45,[7] yayi bikin cika shekaru 50 akan karagar mulki.[8] Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III, Iku Baba Yeye, Alaafin (sarkin) Oyo ya kasance Shugaba na din-din-din na Majalisar Obas da Sarakunan Jihar Oyo har zuwa rasuwarsa ranar Juma'a, 22 ga Afrilu 2022.[9] Salon da aka yi amfani da shi ga Alaafins shi ne; Mai Martaba Sarki.[10]
Welcome to the website of His Imperial Majesty, The Alaafin of Oyo, The Head and Paramount Ruler of the Yorubas.