Alam Baba Lalika | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
1 ga Yuni, 2013 - District: NA-167 Bahawalnagar-II (en)
District: NA-167 Bahawalnagar-II (en) | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Lahore, 12 ga Maris, 1987 (37 shekaru) | ||||||
ƙasa | Pakistan | ||||||
Harshen uwa | Urdu | ||||||
Karatu | |||||||
Harsuna | Urdu | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Addini | Musulunci | ||||||
Jam'iyar siyasa | Pakistan Muslim League (N) (en) |
Alam Dad Lalika ( Urdu: عالم داد لالیکا; an haife shi a ranar 12 ga watan Maris 1987) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan daga watan Agustan 2018 har zuwa Agustan 2023. A baya ya kasance ɗan majalisar tarayya daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018. Shi ɗa ne ga Mian Abdul Sattar Laleka wanda kuma fitaccen jigon PML(N) ne kuma yana kusa da Mian Muhammad Nawaz Sharif. Alam Dad Laleka ya samu karɓuwa sosai a Mazaɓar a farkon shekarun bayan rasuwar mahaifinsa.
An haife shi a ranar 12 ga watan Maris 1987. Ya girma a Lahore, yana ƙarami yana jin daɗin motoci kuma yana sha'awar su. Samun fama da mutuwar mahaifinsa musamman a lokacin yana ƙarami da kuma ɗaukar nauyin da ke tattare da shi babban ƙalubale ne.[1]
An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (N) (PML-N) daga Mazaɓar NA-189 (Bahawalnagar-II) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013.[2][3][4][5][6] Ya samu ƙuri'u 95,060 sannan ya doke Mian Mumtaz Ahmad Matyana, ɗan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).[7] A lokacin da yake zama ɗan majalisar tarayya ya taɓa riƙe muƙamin sakataren sadarwa na majalisar tarayya.[8]
A cikin watan Afrilun 2018, an ba da rahoton cewa ya bar PML-N amma wannan rahoton ya zama na bogi.[9] Sai dai ya yi watsi da iƙirarin.[10]
An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar NA-167 (Bahawalnagar-II) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2018 .[11]