Alani Bankole

Alani Bankole
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Baptist Boys' High School
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Chief Suarau Olayiwola Alani Bankole, (an haife shi ranar 17 ga watan Satumba, 1941) ɗan kasuwan Egba ɗan Najeriya ne kuma jigo daga jihar Ogun.Ya kasance shugaban West African Aluminum Products Plc.[1] Yana riƙe da sarautar Yarabawa na Oluwo na Iporo Ake da Seriki Jagunmolu na Egbaland.[2]

Ilimi da rayuwar sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Tsohon dalibi ne a babbar makarantar sakandare ta Baptist Boys da ke Abeokuta Inda ya kammala karatunsa na sakandare.[3] Ya auri Atinuke Bankole, Ekerin Iyalode na Egbaland, tare da sauran matansa; ɗan su Dimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai ne.[2] Shi ne kuma wanda ya kafa kamfanin (Freight Agencies Nigeria Ltd), kamfanin jigilar kayayyaki na farko a yammacin Afirka. Wasu daga cikin muƙarraban sa sun haɗa da, Cif Sanya Abiola Shugaban Kamfanin (Altimax Metal Industries) da wasu shugabannin masana’antu da gwamnoni da Sanatoci da ƴan majalisar wakilai da dama.

Ya kasance ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a lokuta daban-daban guda uku;[4] ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) a shekarar 1979[5] da kuma a shekarar 1983, amma sai aka maye gurbinsa da Soji Odunjo a karshen shekarar. Ya shiga jam’iyyar National Republican Party (NRC) a shekara ta 1989, sannan ya zama mamba a jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP). Ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa[6] sannan ya zama shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa kafin ya bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP a shekara ta 2000.[2]

A shekarar 2004 ya yi hasashen sake fasalin siyasar Najeriya inda jam’iyyun ANPP, PDP da Alliance for Democracy (AD) za su wargaje, sauran kuma za su sake haduwa a matsayin jam’iyyu biyu.[7]

  1. Odebode, Niyi (2007-08-16). "MAN backs NIPC on investment issues". Punch Online. Missing or empty |url= (help)
  2. 2.0 2.1 2.2 Adeyemo, Ademola (2007-11-02). "Bankole the Father…". Thisday online. Leaders & Company. Archived from the original on 2007-11-03. Retrieved 2007-11-04.
  3. Folarin, Dare (2004-01-24). "It's 81 Years of BBHS!". Thisday online. Leaders & Company. Archived from the original on 2005-12-04. Retrieved 2007-11-04.
  4. Bamidele, Yemi (2007-11-07). "My son won't be a stooge –Bankole's father". Daily Trust online. Archived from the original on 2007-08-30. Retrieved 2007-11-17.
  5. Okoror, Fred. "Ex-ANPP chief, Bankole, backs emergency rule". The Guardian. BNW. Archived from the original on 2005-11-10. Retrieved 2007-11-04.
  6. Adebayo, Moshood (2007-11-02). "Dimeji can't afford to fail – Father". The Sun News On-line. The Sun Publishing. Archived from the original on 2008-02-29. Retrieved 2007-11-03.
  7. Oyinlola, Muyiwa (2004-07-03). "PDP, ANPP and AD will break-up and fuse into two parties – Bankole, PDP chief". The Sun. BNW. Archived from the original on 2008-04-03. Retrieved 2007-11-04.