Albert Ebossé Bodjongo

Albert Ebossé Bodjongo
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Kameru
Suna Albert
Shekarun haihuwa 6 Oktoba 1989
Wurin haihuwa Douala
Lokacin mutuwa 23 ga Augusta, 2014
Wurin mutuwa Tizi Ouzou (en) Fassara
Sanadiyar mutuwa accidental death (en) Fassara
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Matsayin daya buga/kware a ƙungiya Ataka
Work period (start) (en) Fassara 2008
Work period (end) (en) Fassara 2014
Wasa ƙwallon ƙafa
Albert Dominique Ebossé

Albert Dominique Ebossé Bodjongo Dika (6 Oktobar 1989 - 23 ga Agustan 2014 ), ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan Kamaru wanda ya taka leda a Kamaru, Malaysia da kuma Aljeriya.

Bodjongo ya taka leda tare da kulob ɗin Douala Athletic Club na garinsu, kulob a MTN Elite Two, Kamaru ta Kasa ta Biyu. Ya kuma buga wa Coton Sport FC da Unisport Bafang a Kamaru.

Ƙungiyar Perak FA ta Malaysia ta sanya hannu a ranar 15 ga watan Afrilun 2012 a matsayin wanda zai maye gurbin ɗan wasan mai fita Lazar Popović . Ya buga wasansa na farko a gasar Laliga a Perak a wasan da suka tashi 2–2 da Sabah FA a ranar 17 ga Afrilun 2012 kuma ya ci ƙwallonsa ta farko a ƙungiyar a wasan da suka tashi 2–2 da Terengganu FA a ranar 4 ga Mayun 2012.

A cikin Yulin 2013, Bodjongo ya sanya hannu don JS Kabylie (JSK). Shi ne ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a gasar Algeria a shekarar 2014 da ƙwallaye 17.

An ruwaito Bodjongo ya buga wasa shida tare da tawagar ƙwallon ƙafar Kamaru (mafi yawan kungiyar ‘B’), kuma ya buga wa tawagar 'yan ƙasa da shekaru 20 a shekarar 2009.

  • Jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa da suka mutu a lokacin da suke wasa

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]