Ali bin Saeed bin Samikh Al-Marri[1] Dan asalin kasar Qatari ne mai kare hakkin dan adam [2] kuma babban ɗan siyasa [3] wanda aka haife shi a ranar 30 ga watan Nuwamba, shekara ta 1972.An nada shi Ministan Kwadago na Jihar Qatar a ranar 19 ga watan Oktoba, shekara ta alif dubu biyu da a shirin da daya 2021, kuma a sake nada shi Minista na Kwadago ta hanyar umarnin Amiri a watan Maris a shekara ta alif dubu biyu da a shirin da ukku 2023. [4][5] Kafin ya hau matsayin ma'aikatar, ya jagoranci Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam na Kasa (NHRC) na Jihar Qatar tun shekara ta alif dubu biyu da tara 2009. [6] Ya kuma yi aiki a matsayin mukaddashin shugaban kasa da sakatare-janar na Global Alliance of National Human Rights Institutions kuma a matsayin shugaban Cibiyar Larabawa ta Cibiyoyin Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa.[7] A shekara ta alif dubu biyu da sha biyu 2012 an zabe shi shugaban kwamitin Larabawa na dindindin kan 'yancin Dan Adam na Ƙungiyar Larabawa da kuma shugaban kungiyar Asiya ta Pacific a shekara ta alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 zuwa shekara ta alif dubu biyu da sha biyar 2015.[8][9] A sake zabarsa a matsayin shugaban NHRC na Jihar Qatar a shekarar alif dubu biyu da goma sha tara 2019.[10][11] A watan Yunin kuma na shekara ta alif dubu biyu da a shirin da ukku 2023, an zabi Al-Marri a matsayin shugaban taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya.[12][13][14]
Dokta Ali Bin Samikh Al-Marri tana da Ph.D. a kimiyyar siyasa a shekara ta alif dubu biyu da shidda 2006, kuma yayi MA a bangaran Kimiyya da Siyasa a shekara ta alif dubu biyu da biyu 2002 da kuma Bachelor na Kimiyya na Siyasa a shekarar 1997. [15]