Alphonse Kotiga | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Cadi |
Karatu | |
Harsuna |
Larabci Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da soja |
Kanar Alphonse Kotiga, wanda aka fi sani da Kotiga Guérina, hafsa ne na sojan Chadi kuma ɗan siyasa. Ya kuma kasance ɗaya daga cikin shugabannin juyin mulkin da ya kaiga hambarar da shugaban kasar Chadi François Tombalbaye, a ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 1975, sannan ya zama minista a gwamnatin sabon shugaban, Félix Malloum.
Dan asalin ƙabilar Moyen-Chari ne da ya koma kudancin Chadi bayan da gwamnatin Malloum ta ruguje a shekarar 1979. A can ya zama shugaban wata kungiyar adawa mai dauke da makamai, Red Codos, amma an sasanta shi da gwamnatin Hissène Habré a 1986.