Améleté Abalo | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Lomé, 7 ga Maris, 1962 | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Togo | ||||||||||||||||||||||||||
Mutuwa | Cabinda (en) , 9 ga Janairu, 2010 | ||||||||||||||||||||||||||
Yanayin mutuwa | kisan kai | ||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football manager (en) | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka |
Pascal Amélété Abalo Dosseh (7 Maris 1962 – 9 Janairu 2010) shi ne mataimakin kocin tawagar kwallon kafa ta Togo[1] kuma manajan kulob ɗin ASKO Kara. [2]
Abalo ya fara aikinsa da kulob ɗin Le Dynamic togolais. Daga shekarar 1982 zuwa 1990, ya taka leda a Championnat National na Togo a matsayin dan wasan kulob ɗin ASKO Kara. [3]
Daga shekarar 2004 har zuwa rasuwarsa, ya horar da ASKO Kara.[4] Bugu da kari, ya yi aiki a matsayin mataimakin koci na kungiyar kwallon kafa ta kasar Togo tun daga shekarar 2006.[5]
An kashe shi ne a wani hari da kungiyar 'yan ta'adda ta Front for the Liberation of the Enclave of Cabinda ta kai wa tawagar kwallon kafar kasar Togo hari a lokacin da yake tafiya gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2010.[6]