Amadou Salifou ɗan siyasan ƙasar Nijar ne wanda ya kasance Shugaban Majalisar Dokokin Nijar daga shekarata 2014 zuwa 2016.[1][2]
Salifou Zarma ne daga yankin Yamai na Goudel. An zabe shi ga Majalisar Dokoki ta ƙasa har sau uku. Salifou ya kuma yi aiki sau biyu a matsayin shugaban majalisar Yamai.
An dakatar da Salifou daga kungiyar ci gaban al'umma ta shekarata 2013 saboda goyon bayan shugaban Nijar Mahamadou Issoufou . A ranar 24 ga Nuwamba, shekarar 2014, kwanaki huɗu bayan da Kotun Tsarin Mulki ta cire Hama Amadou daga mukaminsa na Shugaban Majalisar Ƙasa, aka zabi Salifou ya maye gurbin Amadou; ya samu kuri'u 71 daga cikin 113 daga wakilan majalisar dokokin ƙasar.
Salifou ya rasa kujerarsa a babban zaɓen shekarar 2016 . Ousseini Tinni ya maye gurbinsa a matsayin shugaban majalisar ƙasa a ranar 25 ga Maris din shekarar 2016.[3]