Aminata Ouédraogo | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Burkina Faso |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ouagadougou |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta |
Mamba | Panafrican Film and Television Festival of Ouagadougou |
Aminata Ouédraogo 'yar fim ce kuma mai kula da harkokin fina-finan Burkinabe. Ita ce babban jami'in gudanarwa na kungiyar mata ta Pan-African Women in the Image Industry (UPAFI). [1]
Ouédraogo tayi karatu a Institut Africain d'Education Cinématographique (INAFEC), makarantar fina-finai a Jami'ar Ouagadougou, kafin ta yi karatu a Institut du Multimedia et Architecture de la Communication (IMAC) a Paris. [1]
Ouédraogo ta shawarci Panafrican Film and Television Festival of Ouagadougou (FESPACO). A shekarar 1991, a FESPACO karo na 12, ta kirkiro kungiyar kwararrun mata na Afirka a Cinema, Talabijin d nea Bidiyo (AFAPCTV).[2] A cikin shekarar 1995 an sake fasalin AFAPCTV a matsayin Ƙungiyar Mata ta Afirka ta UPAFI, tare da Ouédraogo a matsayin babbar mai gudanarwa.[3] Ita ce mai ba da shawara ta fasaha ga ministar al'adu da yawon shakatawa a Burkina Faso.[3]