![]() | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | mace |
Ƙasar asali | Honduras |
Wurin haihuwa |
Santa Elena (en) ![]() |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Kyauta ta samu |
Front Line Defenders Award (en) ![]() |
Ana Mirian Romero ƴar fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam ta Honduras ce wacce ta ci lambar yabo ta Front Line Defenders Award a cikin shekara ta 2016.
Romero mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam ce da ke zaune a Santa Elena, La Paz, Honduras.[1] She a member of the Lenca Indigenous Movement[1] Ita mamba ce ta Lenca Indigenous Movement shugabar Majalisar Indigenous ta San Isidro Labrador.[2]
Ta yi kamfen a kan madatsar ruwa mai amfani da wutar lantarki, ta damu da tasirinta ga albarkatun ƙasa.[3] Shawararta ya sanya ta zama barazanar kisa[2] da kuma tashin hankalin ƴan sanda, ciki har da a cikin Oktoba 105 lokacin da aka kai hari gidanta.[1]
Romero ta lashe lambar yabo ta Front Line Defenders Award a cikin shekara ta 2016.[4] Tsohuwar shugabar ƙasar Ireland Mary Robinson ta ba ta kyautar a ranar 9 ga watan Yuni a Dublin.[3] Tafiya zuwa Ireland ita ce balaguron farko da ta yi a duniya.[1]
Romero tana zaune tare da mijinta[5] kuma tana da ƴaƴa biyar, ciki har da ƴar da aka haifa a shekara ta 2016.[3]