Anam Imo | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Jahar Kaduna, 30 Nuwamba, 2000 (24 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||
Tsayi | 170 cm |
Anam Imo (an haifeta ranar 30 ga watan Nuwamban shekaran 2000), itace yar wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya wacce a yanzu haka take buga wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Rosengard na garin Damallsvenskan . Ta kuma wakilci kungiyar kwallon kafa ta kasar Najeriya a matakin mata masu buga kwallo na kasa da yan shekaru 20 .[1]
A watan Maris na shekarar 2016, Imo ta zura kwallo daya tilo a cikin ragan kungiyar kwallon kafa ta Amazons ta Nasarawa, a wasan da suka sha kashi a hannun Najeriya karkashin kungiyar yan kwallan kafan Najeriya na yan shekaru 17, wanda hakan ya faru ne a cikin shirye-shiryen gasar cin kofin kwallon kafa ta mata ta duniya na yan kasa da shekaru 17 .[2]
Jihar Imo an gayyace su su buga wasan a cikin tawagar yan kwallan Najeriya, wannan gayyace daga babban kwach Christopher Danjuma. [3] A lokacin wannan kamfen dinne taci kwallo. [4]A lokacin gasar kofin kwallan kafa na 2016 mai suna Africa Women Cup of Nations, Imo suna cikin wadanda suka samar da babbar hadi a cikin tawagar su, wanda Florence Omagbemi ne ya hado tawagar.[5][6]
Kociya Thomas Dennerby ne ya sanya ta cikin jerin 'yan wasan karshe zuwa Kofin Matan WAFU na 2018 . A gasar, ta zira kwallaye a ragar kungiyar matan Togo a wasan karshe na rukuni. A watan Afrilu na 2018, Imo tana cikin sahun farko a wasan da Najeriya ta sha kashi a hannun Faransa a wasan sada zumunci a Le Mans.[7]