| ||||
Iri | Annoba | |||
---|---|---|---|---|
Bangare na | COVID-19 pandemic by country and territory (en) da COVID-19 pandemic a Africa | |||
Kwanan watan | 19 ga Maris, 2020 – | |||
Wuri | Nijar | |||
Ƙasa | Nijar | |||
Sanadi | Koronavirus 2019 |
Annobar Koronavirus ta shiga Nijar a watan Maris shekara ta 2020. Kungiyar kare hakkin dan'adam ta "Amnesty International" ta fitar da rahoton cewar an sha ka yanjarida dangane da Koronavirus.[1]
Ranar 12 ga watan Janairu shekara ta 2020, hukumar lafiya ta dunya t sanar da faruwar annobar a birnin Wuhan na kasar Sin wadda itama ta samu rahoton bullar ta a 31 Disamban, shekara ta 2019.[2][3]
Samun yaduwar cutar yayi kasa sosai aka cutar SARS a shekara ta 2003, [4][5] amma a sannu annobar ta COVID-19 na kara yaduwa da zama sanadiyyar rasa rayuka.[6][4]
Ranar 19 ga watan Maris,aka samu bullar farko ta anmobar COVID-19 a birnin Niamey, inda aka samu wani dan shekara 36 daga Najeriya. Ya shirya tafiya ne zuwa biranen Lomé, Accra, Abidjan da Ouagadougou.[7]
Biyo bayan haka aka sanar da rufe filayen jiragen Zinder dana Niamey domin kaurace ma yaduwar annobar.[7]
An samu bullar annobar ta Koronavirus ranar 16 ga watan Maris lokacin da wata yar kasar Brazil ta shiga kasar.[8]
Ranar 24 ga watan Maris Nijar ta sanar da samun mutum bakwai dauke da cutar hadi da mutuwar wani daya mai dauke da cutar ta COVID-19.[9]. Mutuwar ta faru ne a Niamey babban birnin kasar, inda wani dattijo dan shekara 63 dan kasar Nijar ya rasu.[10]