Asabe Vilita Bashir | |||
---|---|---|---|
9 ga Yuni, 2015 - District: Damboa/Gwoza/Chibok | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Borno, 19 ga Faburairu, 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Maiduguri academic degree (en) Master of Education (en) : karantarwa academic degree (en) Digiri a kimiyya : karantarwa academic degree (en) Doctor of Philosophy (en) | ||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Asabe Vilita Bashir (an haifeta a ranar 19 ga watan Faburairu, shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyar 1965A.c) a ƙauyen Limankara da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar gwoza,ta kasance mace yar siyasa a Najeriya. An zaɓe ta a matsayin mace mai wakiltar Gwoza, Chibok da ke jihar Borno. Yar siyace a ƙarƙashin jam'iyyar APC dake wakiltan Gwoza, Chibok da kuma Damboa na jihar Borno. Ta kuma goyi bayan samar da adalci ga majiyatan rikicin Boko Haram.
Bashir ta karɓi takardar shedar karatun ta na GCE daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Maiduguri a shekarar 1984. Daga nan sai ta shiga Jami'ar Maiduguri don karatun koyarwa. An ba ta sakamakon BSc na Koyarwa (Education) a cikin shekarar 1988, da MEd a Gudanarwa da Tsare-tsare a shekarar 1992, da kuma Ph.D. a cikin Falsafa a shekarar 2002.[1]
Ta kasance mamba a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya,[2] wakiltar mazabar Gwoza, Chibok da Damboa a jihar Borno .[3] Tana yin shawarwari kan aikin da zai inganta rayuwar wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, musamman mata da yara.[4][5]