Asibitin Koyarwa na Jami'ar Olabisi Onabanjo | |
---|---|
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Olabisi Onabanjo University Teaching Hospital |
Iri | university hospital (en) , medical organization (en) , Asibiti da medical facility (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Mamallaki | Jami'ar Olabisi Onabanjo |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1986 |
oouth.com… |
Asibitin Koyarwa na Jami'ar Olabisi Onabanjo (OOUTH), (wanda ake kira da, Asibitin Koyarwa na Jami'ar Jihar Ogun (OSUTH), yana cikin Sagamu, Jihar Ogun, Kudu maso Yammacin Najeriya.[1] An kafa asibitin koyarwa ne a shekarar 1986 da manufar koyar da ɗaliban likitanci daga jami’ar Olabisi Onabanjo da kuma samar da ayyukan kiwon lafiya ga ƴan asalin jihar Ogun da Najeriya baki ɗaya.[2]
An kafa OOUTH a ranar 1 ga watan Janairu, 1986, tare da haɗin gwiwar Kwalejin Kiwon Lafiyar Kwalejin Obafemi Awolowo don ba da horon likitanci ga ɗaliban da ke karantar aikin likitancin a Jami'ar Olabisi Onabanjo. Asibitin koyarwa ya kasance a tsohon asibitin jihar, Sagamu, jihar Ogun, Najeriya. Babban Daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin shi ne Farfesa. AAO Laditan. Majalisar gudanarwar da gwamnatin jihar ta naɗa ne ke kula da asibitin.[3] Ya zuwa shekarar 2016, shugaban majalisar gudanarwar shine Farfesa Emmanuel O. Otolorin.[4]