Aster Yohannes | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1950s (64/74 shekaru) |
ƙasa | Eritrea |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Petros Solomon (en) |
Karatu | |
Makaranta |
University of Phoenix (en) Jami'ar Addis Ababa |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | People's Front for Democracy and Justice (en) |
Aster Yohannes tsohuwar ‘yar jam'iyyar Eritrean People's Liberation Front (EPLF) ce kuma mai fafutukar 'yancin kai. Bayan samun 'yancin kai, ta yi aiki a ma'aikatar Kifi da albarkatun ruwa a shekarar 1995. Ita kuma matar dan siyasan Eritrea da aka tsare Solomon Petros ce.
Ma'aikatan tsaro sun tsare ta a Filin jirgin saman Asmara da ke babban birnin Asmara a ranar 11 ga watan Disamba na shekara ta 2003, lokacin da ta dawo bayan karatun shekaru uku a Jami'ar Phoenix don haɗuwa da 'ya'yanta. Ba a san inda take ba tun wancan lokacin. Petros da Aster suna da 'ya'ya hudu.