Auwal H Yadudu

Auwal H Yadudu
Rayuwa
Haihuwa Jahar Katsina, 1953 (70/71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Harvard Law School (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Hausa
Turanci
Sana'a
Sana'a Malami da malamin jami'a

Auwal Yadudu (An haife shi a shekara ta 1953) malanta ne a Nijeriya.[1] Malamin lauya ne kuma Mataimakin Shugaban Jami'ar Tarayya na yanzu, Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, Nijeriya.

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Yadudu a garin Funtua na jihar Katsina. Ya yi difloma a fannin shari'a a shekara ta 1978 daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Ya ci gaba da samun digiri na Dokoki a can a cikin shekara ta 1979. Daga baya ya sami Master of Laws (LLM) a shekara ta 1982 da Doctor of Judicial Science daga Harvard Law School a Amurka a shekara ta 1985.

Ya yi aiki a matsayin Shugaban Kwalejin Shari'a a Jami'ar Bayero. A shekara ta 2016 ya zama Mataimakin Shugaban Jami'ar Tarayya, Birnin Kebbi, Jihar Kebbi. Yadadu ya kasance a matsayin mai ba da Shawara kan Harkokin Shari'a ga Marigayi Shugaban kasa, Janar Sani Abacha. Ya kuma yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasa na Tsaro kan Doka, Shari'a da 'Yancin Dan Adam.

  1. dnladmin (2017-02-16). "Prospective JSC – Personality Check: Prof. Auwalu Hamish Yadudu". DNL Partners. Retrieved 2021-09- 24.3