Azmi Mohammed Magahed | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Dakahlia Governorate (en) , 15 ga Afirilu, 1950 |
ƙasa |
Kingdom of Egypt (en) Republic of Egypt (en) United Arab Republic (en) Misra |
Mutuwa | Dokki (en) , 12 Satumba 2020 |
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Koronavirus 2019) |
Ƴan uwa | |
Yara |
view
|
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | volleyball player (en) da mai gabatar wa |
Mahalarcin
| |
Tsayi | 1.89 m |
Azmi Mohamed Megahed ( Larabci: عزمي محمد مجاهد ; 15 Afrilu 1950 – 12 Satumba 2020) ɗan wasan ƙwallon raga ne na ƙasar Masar. Ya yi takara a gasar maza a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 1976.[1]
An haife shi a Dakahlia,[2] Megahed ya taka leda a Zamalek SC da kuma kungiyar Masar ta kasa tsawon shekaru 16. Ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka a 1974. [3] Ya kuma lashe lambobin yabo na mutum daya da na gida da na nahiya da dama a matsayinsa na dan wasa da manaja.[4] Daga baya ya zama mamban kwamitin Zamalek SC, sannan ya yi aiki a matsayin mai sharhi kan harkokin siyasa kuma mai gabatar da shirye-shiryen talabijin a "Al Assema TV".[5] Ɗansa, Amir Azmy, ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa. [3]
Ya mutu a ranar 12 ga watan Satumba, 2020 a wani asibiti a Alkahira sakamakon COVID-19 yayin barkewar cutar a Masar.