Bakari Mwamnyeto | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Tanzaniya, 1995 (28/29 shekaru) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Bakari Nondo Mwamnyeto (an haife shi a ranar 5 ga watan Oktoba 1995) kwararren dan wasan kwallon kafa ne dan Kasar Tanzaniya wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga Matasan Afirka da Kungiyar kwallon kafa ta Tanzaniya.
Mwamnyeto ya fara babban aikinsa na wasa tare da kungiyar Coastal Union a gasar Premier ta Tanzaniya, daga karshe ya zama kyaftin dinsu.[1] Ya koma cikin Matasan Afirka a ranar 14 ga Agusta 2020.[2]
Mwamnyeto ya fara wasansa na farko tare da tawagar kasar Tanzaniya a wasan sada zumunci da suka yi da Rwanda a ranar 14 ga Oktoba 2019.[3] Ya kasance cikin tawagar 'yan wasan da aka kira zuwa gasar cin kofin kasashen Afirka na 2020.[4]