Bakin Tekun Kuramo | ||||
---|---|---|---|---|
bakin teku | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jahar Legas |
Bakin Tekun Kuramo,wani gaɓar teku ne da ke da yashi a Legas, Najeriya, yana gefen kudancin Tsibirin Bictoriyal, gabas da Bar Beach da kudu da tafkin Kogin Kuramo.[1] Ya kasance wurin da gidaje da rumfuna da yawa waɗanda suke ba a bisa ƙa'ida ba, wasu daga cikinsu ana amfani da su don nishaɗin kiɗa, kide, mashaya da karuwanci.[2][3] A watan Agustan shekarar 2012, ruwan tekun Atlantika ya yi kaca-kaca a gabar tekun Kuramo, inda ya lalata wasu rumfunan gidaje tare da kashe mutane 16.[4] Washegari hukumomin gwamnati suka kwashe yankin, suka rusa sauran rumfunan sannan suka fara cika yashi.[5]
An ce ambaliya na aukuwa a bakin tekun na faruwa ne a duk watan Agusta a bakin teku, ko da yake a shekarun baya ba a rasa rayuka ba.[6]