Banco di Roma | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | kamfani da banki |
Masana'anta | financial sector (en) |
Ƙasa | Italiya |
Mulki | |
Hedkwata | Roma |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1880 |
Founded in | Roma |
Dissolved | 1992 |
Banco di Roma ya kasance bankin Italiyanci da ke Rome, yankin Lazio. An kafa shi ne a ranar 9 ga watan Maris shekara ta 1880.
Tare da Credito Italiano da Banca Commerciale Italiana an dauke su a matsayin bankin bukatun ƙasa. A 1991 bankin ya hade da Banco di Santo Spirito da Cassa di Risparmio di Roma don kafa Banca di Roma, [1]magabacin Capitalia (wanda UniCredit ya siya a shekarar 2007).
Banco di Roma ya kuma mallaki kusan kaso 30% na hannun jarin bankin Belgium a shekarar 1989. Banco di Roma (Belgio) SA, ya samo asali ne daga Monte dei Paschi di Siena (MPS) a 1992.
Banco di Roma kuma ya sayar da Banco di Perugia ga Banca Toscana, reshen MPS a shekarar 1990. [2][3][4]