Batile Alake | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Batile Alake |
Haihuwa | Ogun, 20 century |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 10 ga Augusta, 2013 |
Karatu | |
Harsuna |
Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi |
Kayan kida | murya |
Batile ko Batili Alake (ta mutu a shekara ta 2013) shahararriyar mawaƙiya ce a Nijeriya.[1][2]
Batile Alake haifaffiyar Ijebu Igbo ne, a jihar Ogun . Alhaja Batile Alake ta mutu a shekarar 2013, tana da kimanin shekara 78. Ba a san ainihin shekarunta ba. [3]
Alake tayi fice a fannin waƙoƙin addinin Islama, irin na Yarbawa ta hanyar yin kiɗe-kiɗe da wake-wake a duk fadin kasar Yarbawa, kuma itace mawaƙiya ta farko da ta fara haɗa kundin Waƙoƙi. Ta kasance mai aiki sosai a lokacin 1950s da 1960s.