Benafsha Yaqoobi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Afghanistan, |
ƙasa | Afghanistan |
Sana'a | |
Sana'a | disability rights activist (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Benafsha Yaqoobi (wanda kuma aka fi sani da Benafsha Yaqubi ) 'yar fafutukar kare hakkin naƙasassu ta Afghanistan. An sanya ta ɗaya daga cikin mata 100 na BBC a shekarar 2021.
An haifi Benafsha Yaqoobi makahuwa a Afghanistan kuma ta zama mai fafutukar kare hakkin naƙasassu. Ta yi karatun adabin Farisa a Iran sannan ta yi digiri na biyu a Kabul, kafin ta yi aiki a ofishin babban mai shari'a. [1] Tare da mijinta Mahdi Salami, wanda shi ma makaho ne, ta kafa kungiyar Rahyab Organisation don taimakawa da ilmantar da makafi. [1]
Daga shekarar 2019 zuwa gaba, Yaqoobi ta kasance kwamishiniya a hukumar kare hakkin ɗan Adam mai zaman kanta ta Afganistan (AIHRC) har zuwa lokacin da ta gudu tare da mijinta a ƙasar Afganistan a shekarar 2021 bayan kungiyar Taliban ta sake karɓar mulki. A yunkurinsu na uku na tashi, sun isa filin jirgin saman Kabul kuma sun yi tafiya zuwa Burtaniya.[2]
Yakubi da mijinta, waɗanda dukkansu na fama da matsalar gani, sun kafa Rahyab, da nufin samar da ilimi da kuma gyara ga naƙasassu a Afganistan. Ita ma mai fafutukar kare hakkin bil adama Benafsha Yakubi ta yi aiki a hukumar kare hakkin ɗan Adam mai zaman kanta ta ƙasar kuma ta yi aikin koyar da yara masu naƙasar idanu.[3]
A cikin shekarar 2020, Yaqoobi ta kasance 'yar takarar kwamitin kare hakkin nakasassu. [4] An sanya ta ɗaya daga cikin mata 100 na BBC a shekarar 2021. [5]