Bent Familia | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1997 |
Asalin suna | بنت فاميليا |
Asalin harshe | Larabci |
Ƙasar asali | Tunisiya |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
During | 105 Dakika |
Launi | color (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Nouri Bouzid |
Marubin wasannin kwaykwayo | Nouri Bouzid |
'yan wasa | |
Samar | |
Mai tsarawa | Ahmed Bahaeddine Attia (en) |
Director of photography (en) | Armand Marco (en) |
External links | |
Bent Familia wani wasan kwaikwayo ne da aka shirya shi a shekarar 1997 da aka shirya a Tunisiya game da Amina (Leila Nassim) wata mata musulma mai aure da ke zaune a Tunis tare da 'ya'yanta mata biyu. Ko da yake an ba ta wasu ’yanci a matsayinta na mace musulma hakan yana tauyewa idan ta haɗu da tsohuwar kawarta daga makaranta mai suna Aida wadda (Amel Hédhili) ta yi.[1]
Mahaifiyar 'ya'ya biyu, Aida ta tsaya tsayin daka don kada ta amince da rashin amincewar mijinta. An sake ta (Auren ta ya mutu) kuma ta ɗauki kanta a matsayin mace mai 'yanci. Sai kuma kawarsu Fatiha (Nadia Kaci), wata hamshakiyar da ta dage cewa za ta bar Tunis ta zauna a Yamma. Wannan ƙaƙƙarfan abokantaka na barazana ga mijin Amina, Majid (Raoul Ben Amor), wani mazinaci da ke ƙoƙarin kawo wa ƴancin al'ummar musulmi rauni a kanta. Nouri Bouzid ne ya ba da umarni, wannan fim ɗin da aka ɗauka da kyau yana gabatar mana da ainihin matsalolin mata a Arewacin Afirka na wannan zamani, amma ba ya ba da mafita mai sauƙi.[2]