| ||||
Iri |
film festival (en) ![]() | |||
---|---|---|---|---|
Validity (en) ![]() | 1995 – | |||
Wuri | Vesoul | |||
Ƙasa | Faransa | |||
Yanar gizo | cinemas-asie.com | |||
![]() ![]() ![]() |
Bikin fina-finan Asiya ta Duniya a Vesoul (Faransanci: Festival international des cinémas d'Asie ) bikin fina-finai ne na musamman na shekara-shekara wanda ke mai da hankali kan sinimar Asiya. Ana kuma gudanar da bikin ne duk shekara a birnin Vesoul da ke ƙasar Faransa. Martine da Jean-Marc Thérouanne ne suka ƙirƙira bikin a shekarar 1995 waɗanda ke jagorantar bikin tun daga lokacin.[1][2]
ƙololuwar kyauta a bikin itace lambar yabo ta Golden Cyclo. Sauran kyaututtukan sun haɗa da lambar yabo ta Musamman na Harsuna "O" Award, wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Gabas da Wayewa ta ƙasar Faransa ke bayarwa, da kuma lambar yabo ta Emile Guimet ta Ƙungiyar Abokan Tarihi na National Museum of Asian Arts-Guimet a bikin.[3]
A karo na 17 na bikin, wanda ya jawo hankalin masu kallo kimanin 28,700, an ba da kyautuka uku ga fim din ƙasar Sin mai suna "Addiction to Love" na darekta Liu Hao . Fim ɗin ya sami lambar yabo mafi girma da kuma lambar yabo ta "O" da kuma Guimet. An raba kyautar Golden Cyclo da "PS", ga darektan Uzbekistan Elkin Tuychiev.[3]