Chaimae Edinari | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 19 ga Yuli, 1999 (25 shekaru) |
ƙasa | Moroko |
Ƴan uwa | |
Ahali | Lamia Eddinari |
Sana'a | |
Sana'a | judoka (en) |
Mahalarcin
|
Chaimae Eddinari 'yar wasan Judoka ce 'yar ƙasar Morocco.[1] Ita ce ta lashe lambar zinare a wasannin Afirka na shekarar 2019 kuma ta samu lambar tagulla a Gasar Judo ta Afirka ta shekarar 2021.[2] [3]
A shekarar 2018, ta fafata a gasar tseren kilogiram 48 na mata a gasar Judo ta duniya da aka gudanar a Baku, Azabaijan.[4]
Ta fafata a gasar tseren kilogiram 48 na mata a gasar Mediterranean ta shekarar 2022 da aka gudanar a Oran, Algeria.[5]
Shekara | Gasar | Wuri | Ajin nauyi |
---|---|---|---|
2019 | Wasannin Afirka | 1st | -48 kg |
2021 | Gasar Cin Kofin Afirka | 3rd | -48 kg |