![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 471 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Charanchi (ko Cheranchi ) ƙaramar hukuma ce a jihar Katsina, arewacin Najeriya. Garin, akan babbar hanyar A9, shi ne hedkwatar karamar hukumar.[1]Shugaban karamar hukumar shine Dr.Badamasi Lawal Charanchi[2] yawan jama'a ya kai kimanin 79,000 (2003), kuma yankin ya kai 471. 2. [1]
An kafa karamar hukumar ne daga tsohuwar karamar hukumar Rimi a shekarar 1996. A yanzu haka akwai kansiloli 11 da ke wakiltar mazabarsu a harkokin gudanarwar karamar hukumar. Wadannan kansilolin suna da hakkin tsige Shugaban Karamar Hukumar idan aka yi rashin da’a ko almubazzaranci da asusun gwamnati.
Akwai hakimai biyu a karamar hukumar; Sarkin Shanun Katsina Hakimin Charanchi da Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye.
Sauran garuruwan karamar hukumar sun hada da Kuraye, Banye, Radda, Koda, Ganuwa, Yana, sabon Gari da Maje.