Charles Ayo | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Egbe (en) , 31 Oktoba 1958 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Mutuwa | 2 ga Augusta, 2023 |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Ilorin |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Employers |
Trinity University (en) ga Augusta, 2023) Jami'ar Covenant University (2012 - 2016) |
Charles Korede Ayo (ya rayu daga 31 Oktoba 1958 zuwa 2 Agusta 2023) malami ne na Najeriya, mai gudanarwa kuma Shugaban Jami'ar Covenant.[1][2] Kafin ya gaji Aize Obayan a matsayin shugaban jami’ar, ya kasance shugaban sashen nazarin kimiyyar kwamfuta da bayanai. Ya kuma shiga cikin bincike kan batutuwan kwamfuta da sadarwa, kamar kasuwancin lantarki da kwamfuta.[3][4][5] Ayo ya ba da fifiko kan horar da jagoranci a Jami'ar Convenant,[6] da kuma kan aikin ilimi da "Godly Standard."[7] Ya nemi sanya Jami'ar Covenant "daya daga cikin manyan jami'o'i 10 a duniya" cikin shekaru goma.[8][9]
Ayo shi ne dalibin da ya yi fice a fannin Computer Science a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1984. Ya yi digirin digirgir (Ph.D)[5] a Numerical Computation a Jami'ar Ilorin. Kafin ya shiga Covenant, ya koyarwa a Jami’ar Jihar Lagos. Ya yi aure da ‘ya’ya hudu[5] .
A cikin 2017, Ayo ya gabatar da babban jawabi game da sake fasalin tsarin ba da ilimi mai zurfi don ci gaban jarin ɗan adam da sauyi na ƙasa a wurin taron taro na Jami'ar Crawford.[10]
Charles Ayo ya mutu a ranar 2 ga Agusta, 2023, yana da shekaru 64.[11]