Charmaine Pereira marubuciya ce kuma ƙwararriyar mace a jahar Abuja wato binnin taraiyya, dake Najeriya. Ayyukan ta sun shafi tunanin mata, jima'i, ilimin jinsi, da ƙungiyoyin jama'a da jiha. Pereira kuma ita ce mai gudanarwa na Initiative for Women’s Studies a Najeriya.[1] Ita mamba ce ta Tapestry Consulting, kungiyar da ke neman samar da daidaiton jinsi a wuraren aiki a Afirka.
A cikin shekara ta 1991, Pereira ta sami Ph.D. a Psychology of Education daga The Open University.[2]
A cikin 2004, Charmaine Pereira ta haɗa Jacketed Women: Qualitative Research Methodologies on Sexualities and Gender in Africaa tare da Jane Bennett.
Pereira a halin yanzu tana koyarwa a sashin ilimin zamantakewa a jami'ar Ahmadu Bello.[3] Ayyukanta na bincika ƙalubalen da mai bincike ke fuskanta lokacin yin tambayoyi tsakanin al'adu, jinsi, jima'i, doka, da addini.
Pereira, Charmaine. Gender in the Making of the Nigerian University System. James Currey, 2007.
Pereira, Charmaine, editor. Changing Narratives of Sexuality: Contestations, Compliance and Women’s Empowerment. London, New York: Zed Books, 2014.
Charmaine PereiraBennett, Jane, and Charmaine Pereira, editors. Jacketed Women: Qualitative Research Methodologies on Sexualities and Gender in Africa. Tokyo, New York, Paris: United Nations University Press, 2013.
Pereira, Charmaine. “Domesticating Women? Gender, Religion and the State in Nigeria Under Colonial and Military Rule.” African Identities 3.1 (2005): 69-94.