ChatGPT Plus | |
---|---|
subscription business model (en) | |
Bayanai | |
Bangare na | ChatGPT |
Ƙasa | Tarayyar Amurka |
Authority (en) | OpenAI (mul) |
Maƙirƙiri | OpenAI (mul) |
Ranar wallafa | 1 ga Faburairu, 2023 |
Mai haɓakawa | OpenAI (mul) |
Payment types accepted (en) | Visa Electron (en) |
Shafin yanar gizo | openai.com… |
Uses (en) | GPT-4 (mul) |
ChatGPT Plus Ya kasance wata sabis ne na biyan kuɗi don ChatGPT kuma mallakar OpenAI.[1][2] Biyan kuɗi yana ba da dama ga samfurin GPT-4 na OpenAI..[3]
An fara ƙaddamar da ChatGPT azaman samfoti na bincike tare da manufar gano ƙarfi da raunin tsarin, da kuma tattara ra'ayoyin masu amfani domin ƙarin haɓakawa.[4]
Bayan ƙaddamar da shi, miliyoyin masu amfani sun ba da amsa, wanda ke haifar da sabuntawa masu yawa. An yi amfani da dandalin a fannonin ƙwararru daban-daban, kamar tsara abubuwan da ke ciki da gyarawa, ƙirƙirar ra'ayi, taimakon shirye-shirye, da Kuma binciken batutuwa.[4]
Sabis ɗin yana ba masu biyan kuɗi daidaitaccen dama yayin amfani da shi, kuma yana da sauri wajen amsawa, da bada damar fifiko ga sabbin abubuwa, gami da GPT-4 da plugins na ChatGPT masu zuwa.[5]
Da farko, an ƙaddamar da shi a cikin Amurka kawai.[8] A cikin Maris 2023, an ƙaddamar da shi a Indiya.[9]