Chinaza Amadi

Chinaza Amadi
Rayuwa
Haihuwa 12 Satumba 1987 (37 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen, Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Sport disciplines long jump (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Chinazom Doris Amadi (an haife ta a ranar 12 ga watan Satumba shekara ta 1987) 'yar Najeriya ce kuma 'yar wasan tsalle mai tsayi (Nigerian Long Jumper.

Ta lashe lambar tagulla a gasar cin kofin Afrika ta 2006. A gasar cin kofin Afrika ta 2007 ta zo ta hudu, inda ta bata lambar tagulla da tazarar santimita biyu. A gasar cin kofin Afrika ta 2008 ta lashe lambar azurfa.

Mafi kyawun tsallenta na sirri shine 6.43 metres (21 ft 1 in), wanda aka samu a watan Mayun 2007 a Legas.[1]

Ita ce ta lashe lambar zinare a tsalle mai tsayi a gasar wasannin Afirka ta 2015, amma an cire mata wannan lakabin bayan ta gaza yin gwajin magani na methenolone. [2] An dakatar da ita na tsawon shekaru hudu, har zuwa 15 ga watan Satumba, 2019. [3]

  1. 2007 All-Africa Games, women's long jump final Archived 2007-10-10 at the Wayback Machine
  2. Doping ban shock for Nigeria. IOL (2016-01-24). Retrieved on 2016-01-24.
  3. IAAF list of sanctioned athletes