Chris Attoh | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ghana, 17 Mayu 1979 (45 shekaru) |
ƙasa | Ghana |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Damilola Adegbite (2015 - 2017) |
Karatu | |
Makaranta |
Accra Academy New York Film Academy (en) Achimota School Kwame Nkrumah University of Science and Technology Bachelor of Arts (en) : painting |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da dan wasan kwaikwayon talabijin |
Muhimman ayyuka |
Sylvia (en) A Trip to Jamaica Flower Girl Journey to Self Single and Married Sinking Sands (fim) Tinsel (TV series) |
IMDb | nm3906542 |
Chris Attoh (an haife Christopher Keith Nii Attoh; 17 ga Mayu, 1979) ɗan wasan Ghana ne, daraktan fina-finai, mai gabatar da talabijin kuma furodusa. An fi saninsa da "Kwame Mensah" a wasan soap opera na Najeriya Tinsel.[1][2][3]
Ya halarci Kwalejin Fina-finai ta New York, Makarantar Achimota da Kwalejin Accra. A Accra Academy, abokan karatunsa sun haɗa da ɗan kasuwan watsa labaru da kuma rediyo Nathan Adisi. Daga nan ya wuce KNUST inda ya yi karatun digiri na biyu a fannin zane-zane. Daga baya ya tafi Landan don karantar Banki da Securities.[4]
Ya dyauki nauyin 2016 edition na Vodafone Ghana Awards Awards tare da Naa Ashorkor da DJ Black.[5] Shi ne kuma MC na shekarar 2014 edition na FACE List Awards a birnin New York tare da Sandra Appiah.[6]
A baya ya auri Damilola Adegbite, amma an ruwaito cewa an sake ta a watan Satumba na 2017.[7][8] Ya sake yin aure a ranar Asabar 6 ga watan Oktoba 2018 da Bettie Jennifer, wata 'yar kasuwa a Amurka a wani biki na sirri a Accra.[9]