Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Claire Berlinski | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kalifoniya, 1968 (55/56 shekaru) |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Karatu | |
Makaranta | Balliol College (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida, Marubuci da marubuci |
berlinski.com |
Claire Berlinski (an haifeta a shekara ta 1968) yar jaridar Amurka ce kuma marubuciya. Haihuwa kuma ta girma a California da wasu sassa na Amurka, ciki harda New York City da Seattle, ta karanta Tarihin Zamani a Kwalejin Balliol, Oxford indata sami digiri na uku a Alakar Duniya . Ta zauna a Bangkok, inda tayi aiki a Asiya Times ; Laos, inda tayi aiki na ɗan gajeren lokaci ga shirin ci gaban Majalisar Dinkin Duniya ; da Istanbul, inda tayi aiki a matsayin 'yar jarida mai zaman kanta. Yanzu tana zaune a Paris .
Berlinski ta rubuta litattafai na leken asiri guda biyu, aiki akan mahimmancin Turai ga muradun Amurka, da kuma tarihin rayuwar Margaret Thatcher mai ban sha'awa amma mai mahimmanci. An buga aikin jaridanta a cikin The New York Times da The Washington Post da sauran wallafe-wallafe.
Ita 'yar marubuci ne kuma mai ilimi David Berlinski kuma cellist Toby Saks, jikar mawaki kuma masanin kida Herman Berlinski, kuma 'yar'uwar marubuci Mischa Berlinski . Ta kasance tana zaune a Istanbul har lokacin zanga-zangar Gezi Park lokacin data yanke shawarar ƙaura zuwa Paris don kusanci da mahaifinta bayan mutuwar mahaifiyarta a shekara ta 2013.