Clarence Olafemi

Clarence Olafemi
Gwamnan jahar kogi

6 ga Faburairu, 2008 - 29 ga Maris, 2008
Ibrahim Idris - Ibrahim Idris
Rayuwa
Haihuwa Mopa-Muro
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Clarence Olafemi ‘yar siyasar Najeriya ce da aka nada a karkashin mukaddashin gwamnan jihar Kogi a watan Fabrairu shekara ta 2008, bayan da aka soke zaben gwamna Ibrahim Idris . Ya mika wa Ibrahim Idris a ranar 29 ga watan Maris shekara ta 2008 bayan Idris ya sake lashe zabe [1].

An haifi Olafemi a karamar hukumar Mopa-Muro ta jihar Kogi. Ya kammala karatunsa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria . Ya kasance dan takarar gwamna na jihar Kwara .

An zabi Olafemi a matsayin dan majalisar dokokin Jihar Kogi mai wakiltar mazabar Mopamuro a watan Afrilu shekara ta 2007 akan dandalin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). A watan Satumban shekara ta 2007, kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kogi da ke Lokoja ta soke zabensa. Ya daukaka kara kan hukuncin, kuma a watan Fabrairu shekara ta 2008, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke hukuncin. A watan Yulin 2008, an kira shi a gaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) domin ya bayyana rawar da ya taka wajen karkatar da naira biliyan 12 na jihar .

  1. Kunle Olasanmi (7 February 2008). "Kogi Speaker takes over as Idris loses appeal". The Nation. Archived from the original on 2009-05-10. Retrieved 2009-12-13.